’Yan Ta’addan ISIS Sun Kashe Mutane Fiye da 70 a Harin da Suka Kai wani Kauye a Jamhuriyar Nijar

Akalla mutane 71 ne suka mutu sakamakon wani mummunan hari da ake zargin ’yan kungiyar ISIS na yankin Sahel (ISIS Sahel) suka kai wa kauyen Manda da ke  yankin Garoul na Tillaberi a yammacin Jamhuriyar Nijar.



Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 8 na dare agogon yankin, a ranar 20 ga Yuni, inda aka kashe mutane da dama ciki har da ‘ya’yan  dagacin kauyen  guda huɗu. Kana an kone gidaje da dama.

Majiyoyi sun ce maharan sun isa kauyen dauke da manyan makamai, inda suka fara harbe-harbe ba kakkautawa tare da ƙone gidaje.

Rahoton ya kuma ce babu jami’an tsaro ko dakarun Forces de Défense et de Sécurité (FDS) da suka kai dauki kauyen  a lokacin harin ko bayan harin.

Wasu da suka tsira daga harin sun bayyana cewa sun kwanta kamar sun mutu a cikin gawarwakin mutanen da aka kashe don kauce wa harbin maharan.

Rahotanni basu tantance musabbabin kai harin ba, yankin Tillaberi ya dade yana fama da tashin hankali daga kungiyoyin  da ke da alaka da ISIS da al-Qaeda, duk da kokarin da ake yi wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Previous Post Next Post