Kungiyar kare haƙƙin Musulmai a Najeriya, Muslim Rights Concern (MURIC), ta bayyana rashin jin daɗinta kan kisan wasu Musulmai da ke kan hanyarsu zuwa bikin aure a jihar Filato.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya caccaki Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da zarginsa da ƙoƙarin rage girman mummunan harin da 'yan kabilarsa suka kai wa matafiyan Musulmi.Kungiyar ta bayyana harin a matsayin “na rashin jin dadi ƙwarai, abin ƙyama, kuma abun Allah wadai da ba za a aminta da shi ba”, yayin da ta bayyana jawabin da gwamnan ya fitar a matsayin wata hanya ta nuna rashin kimanta abinda ya faru.
Kungiyar tace ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya. Wannan hari mai muni, da ya sabawa doka da ɗabi’a kuma abin ƙyama ne.
MURIC ta bayyana yankin da aka kai harin a matsayin fagen kashe Musulmai, musamman matafiya. Ta kuma jaddada cewa matasan yankin sun kasance masu aikata irin waɗannan hare-hare ba tare da nadama ba, kamar yadda tarihi ya nuna cewa a baya an kaiwa Musulmai da dama hare-hare a wannan yanki.
Kungiyar ta ci gaba da sukar gwamna Mutfwang, da kokarin ɓoye girman laifin da aka aikata da dalilin cewa matafiyan sun "bata hanya" ne kuma suka fada cikin "mummunar yanayi mai cike da tashin hankali" a yankin Mangun da ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda.
MURIC ta ce wannan irin bayani daga gwamnan abin damuwa ne, ganin cewa an sha kai irin wannan harin a wannan hanyar da Musulmi matafiya ke amfani da ita, kuma har yanzu gwamnati ba ta dauki matakin da ya dace ba don dakile faruwar irin hakan.