Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta gabatar da tayin fam miliyan £9.3 domin daukar dan wasan tsakiyar Brentford, Christian Norgaard, a cewar rahoton UK Mirror.
‘Yan wasan Gunners na bukatar karfafa bangaren tsakiya a wannan bazarar cinikin ‘yan wasa, tare da kallon Norgaard a matsayin dan wasa mai kyau da ya dace.Dan wasa Jorginho ya koma Flamengo bayan barin Arsenal a matsayin kwantiragin, yayin da makomar Thomas Partey ke cikin halin tsaka mai wuya. Kwantiragin dan wasan Ghana zai kare mako mai zuwa, kuma akwai alamun cewa zai bar kungiyar kwallon.
Arsenal na dab da kammala daukar Martin Zubimendi daga Real Sociedad, bayan sun cimma yarjejeniya da kulob din La Liga. Ana sa ran za a sanar da kammala sayan Zubimendi a mako mai zuwa.
Kazalika Arsenal na ci gaba da bibiyar wasu 'yan wasan da ke kasuwa domin cike gibin da ke tsakiyar fili, yayin da suke shirin fuskantar sabuwar kakar Premier League.