Sabon dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Tosin Adarabioyo, ya bayyana cewa yana dab da yanke hukunci kan kasar da zai wakilta a matakin Kasa.
Dan wasan mai shekaru 27, ya buga wa kungiyoyin matasan Ingila sau 14 a matakai daban-daban. Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta taba tuntubar shi a baya domin sauya kasa.
Sai dai a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa(NAN), Adarabioyo ya ce zai bayyana matsayinsa nan ba da jimawa ba.
Adarabioyo ya ce “Tambaya ce da nake yawan amsawa kwanan nan. Ee, wani abu ne da na ke nazari kuma za a sami amsa a kai a nan gaba,”.
“Zan tattaunawa a kai. Sai mu gani yadda al'amura za su kaya.”
Adarabioyo ya koma Chelsea ne a kakar bazarar nan bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Fulham a matsayin dan kwantiragi.
Tags:
Wasanni
