Dakarun Operation Hadin Kai, Sun Dakile Yunkurin Kai Harin Ta'addanci a Chibok

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani mummunan hari da ake zargin mayakan ISWAP ne suka yi yunkurin kai wa  a kauyen Shikarkir da ke karamar hukumar Chibok, jihar Borno.



Rahotanni  sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kutsa kauyen da misalin karfe 5:20 na yamma, amma sai suka gamu da cikakken turjiya daga dakarun soji tare da hadin gwiwar 'yan sa kai da mafarauta na yankin.

Dakarun sun yi musayar wuta da ‘yan ta’addan har suka tilasta musu janyewa bayan an halaka da dama da ba a iya tantance  adadinsu ba.

Yayin  musayar harbe-harbe, harsashi ya sami wasu fararen hula hudu. Mutane biyu, da wani mai suna  Ishaku Markson mai shekaru 30 da Buba Zakariya mai shekaru 28, sun samu munanan raunuka, kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu a Asibitin Gwamnati na Chibok.

Sauran mutum biyu da suka jikkata a yayin musayar wutar, sun hada da, Yama Wadai  mai shekara 41 da Maina Fali, yanzu haka suna samun kulawa a wannan asibitin, inda ma’aikatan lafiya suka tabbatar da cewa suna samun sauki.

Harin na zuwa a dai-dai lokacin da rundunar Operation Hadin Kai ke kara matsa kaimi wajen murkushe kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Previous Post Next Post