Babban hafsan Sojin Kasa (COAS), Olufemi Oluyede, ya kai ziyara jihar Benue domin dakile kashe-kashen da ake yi

 

Babban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya kai ziyara jihar Benue a ranar Talata a wani yunkuri na musamman domin magance yawan kashe-kashen da ake zargin makiyaya da kungiyoyin wasu miyagun mutane na yi wa mazauna kauyuka  a jihar.

Wata majiya daga Shelkwatar rundunar sojin da ke Abuja ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) cewa COAS yana matukar damuwa kan kashe-kashen da ake yi wa fararen hula da kuma korar mutane daga gidajensu.





Bayanai na cewa Laftanar Janar Oluyede, tare da wasu manyan jami’ai daga shelkwatar sojin, ciki har da manyan jami’an gudanarwa (PSOs), suna kan hanyarsu ta zuwa jihar domin duba halin tsaro da ake ciki.

Majiyar ta bayyana cewa COAS ya bayar da umarnin  tura Karin sojoji da kayan aiki zuwa jihar domin farautar kungiyoyin ‘yan bindiga da ke addabar jama’ar jihar Benue.

Ana sa ran COAS zai gudanar da tarurruka da suka shafi dabarun tsaro tare da dukkan kwamandojin runduna da na sassa domin tattauna hanyoyin kawo karshen rikicin da kuma duba nasarorin da aka samu cikin ayyukan da ake gudanarwa,

Kazalika ana sa ran zai kai ziyara sansanonin sojoji da wuraren aikin rundunar a fadin jihar domin yin magana da dakarun domin kara musu kwarin gwiwa da karsashi wajen yaki.

Previous Post Next Post