Ukraine ta ce ta lalata gadar Rasha zuwa yankin Crimea da aka mamaye

Hukumar tsaron cikin gida ta Ukraine, SBU, ta ce ta kai hari da nakiya a ƙarƙashin ruwa a kan gadar da ke haɗa Rasha da yankin Crimea da ta mamaye, inda ta ce harin ya lalata titin mota da na jirgin ƙasa da ke gadar. Wannan ne karo na uku da Ukraine ke kai wa gadar hari tun bayan fara yaki.


A cewar SBU, sun tayar da nakiya mai nauyin  kilogiram 1,100 (fam 2,420) a safiyar ranar Talata don lalata ginshiƙan gadar da ke ƙarƙashin ruwa a yankin mashigin Kerch, a wani shiri da suka dade suna tsara wa.

 Wata sanarwa da SBU ta fitar ta ce “Mun taba kai harin gadar Crimea sau biyu a shekarar 2022 da 2023. Yanzu mun ci gaba da kai harin ƙarƙashin ruwa,” 

Sanarwar ta kara da cewa. “Gadar yanzu tana cikin wani yanayi na bukatar gaggawa.”

SBU ta saki wani faifan bidiyo da ta ce yana nuna fashewar nakiya a kusa da ɗaya daga cikin ginshiƙan gadar.

Sai dai wasu masharhanta da ke  goyon bayan Rasha sun ce harin bai yi nasara ba, inda suka yi zargin cewa wani jirgin ruwa mai dauke nakiya na Ukraine ne ya kai harin.

Wani shafin Internet na hukuma a Rasha da ke bayar da bayani kan gadar ya ce an dakatar da amfani da ita na kusan awa uku tsakanin ƙarfe 4 na safe zuwa 7 na safe agogon wurin (01:00 zuwa 04:00 GMT), ba tare da bayyana dalili ba. 

Sai dai ya ce an sake bude gadar kuma tana aiki kamar yadda aka saba.

Gadar Crimea mai tsawon kilomita 19 (mil 12) da ke kan mashigin Kerch ita ce kadai hanya kai tsaye  hanyar sufuri tsakanin Rasha da yankin Crimea da Rasha ta mamaye daga  Kasar Ukraine a shekarar 2014.

Gadar na daga cikin muhimman abubuwa na Shugaban Rasha, Vladimir Putin. Gadar na da rassa biyu — daya don motoci, daya don jirgin ƙasa — kuma tana da ginshiƙai da ke goyan ta, da kuma faɗaɗɗen sashe da ke da manyan ƙafafun ƙarfe inda jiragen ruwa ke bi daga Tekun Black sea zuwa Tekun Azov.

An yi amfani da gadar ne a lokacin da sojojin Rasha suka mamaye Ukraine a watan Fabrairun 2022, inda suka shiga Crimea ta gadar sannan suka ci gaba da kwace wasu yankuna kamar Kherson da Zaporizhia.

Harin Rasha a Ukraine

A gefe guda kuma, sojojin Rasha sun kai hari birnin Sumy na Ukraine, inda suka kashe aƙalla mutane uku tare da jikkata da dama, a cewar Ma’aikatar Lafiya.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana cewa wasu rokoki da aka harba ta hanyar amfani da na’urar harba rokoki masu yawa bai fashe ba, inda ya fada cikin wani gini.

A shafinsa na Telegram, Zelenskyy ya ce: “Wannan harin ya isa domin kowa ya fahimci yadda Rasha ke son a kawo karshen wannan yakin.”

A ranar Litinin, Rasha ta shaida wa Ukraine a tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Istanbul cewa za ta daina yakin ne kawai idan Kyiv ta mika wasu sabbin yankuna da kuma amincewa da dakatar da hare-hare kan dakarunta. Ukraine ta sake jaddada cewa wannan ba zai taba yuwuwa ba, 

Ta kuma ce hakan daidai yake da mika wuya.

Previous Post Next Post