Mutum biyu sun mutu bayan da ake zargin an kai harin bam a babban birnin Uganda


Rundunar sojin Uganda ta bayyana cewa mutane biyu sun mutu bayan da aka yi zargin  kai wani  harin bam a wani wurin ibada na Katolika a babban birnin kasar, Kampala.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, Rundunar sojin  sun ce “Sun cafke da  kashe wasu ‘yan ta’adda biyu da ke dauke da makamai” a unguwar Munyonyo, da ke wani yanki na Kampala.



Wadanda suka mutu sun hada da Namiji da Mace da ke kan babur din haya.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Kasar, Kituuma Rusoke, ya ce Matar tana a matsayin fasinja ce kafin abin ya  fashe lokacin da jami’an tsaro da ke bin sawunsu, yayin da  suka kusa cim musu. Rusoke bai bayar da karin haske ba, 

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike.

A yau Talata, Uganda na bikin hutun kasa domin tunawa da wasu  Kiristoci da aka kashe tsakanin 1885 da 1887 bisa umarnin wani sarki a lokacin. Wannan biki na karbar bakuncin  dubban Mutane zuwa wani wuri dabam kusa da Kampala, inda manyan jami’ai ciki har da Shugaban kasa Yoweri Museveni suka halarci taron.

Hare-haren bam ba su cika faruwa a Uganda ba, sai dai hukumomi kan fitar da gargadi a wasu lokuta game da shirin da mayaka ke yi domin tayar da zaune tsaye ga gwamnati mai ci ta Shugaba Museveni.

Previous Post Next Post