Dubban mutane sun hallara a ranar Asabar domin gudanar da sallar jana’izar ba a gaban gawa ba (Salatul Ga'ib)na marigayi attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94.
An gudanar da sallar ne a Masallacin Umar Bin Khattab da ke Dangi a birnin Kano, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa (National Council of Ulama), Sheikh Ibrahim Khalil.
Manyan baki da suka halarta sun hada da jami'an gwamnati da 'yan kasuwa, ciki har da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, da Kwamandan Rundunar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Sauran waɗanda suka halarci jana'izar sun hada da attajirai da wasu fitattun ‘yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati daga fadin jihar nan, da sun shaida addu’ar.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu ne a birnin Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kuma ana sa ran za a binne shi a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.
