Kotun Tarayya da ke Ikoyi, Legas, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a D. E. Osiagor, ta yanke wa wasu 'yan ƙasar Sin guda tara hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan gyaran hali bisa laifin aikata ta'addanci da damfara ta intanet.
Wata sanarwa da Hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon (EFCC) ta fitar a ranar Talata ta shafin X ta bayyana cewa an kama waɗanda aka yanke wa hukuncin ne cikin wani gagarumin samame da hukumar ta EFCC ta gudanar a ranar 19 ga Disamba, 2024.
Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da: LI Dong da Deng Wei Qiang da Huang Bo da Xiong Zhen, sauran sun haɗa da Lai Rui Feng da Zhao Xiao Hui da Lui Hai Rong da Lui Gang da kuma Du Ji Feng.
Ana zargin su da kasancewa cikin 'yan wata ƙungiya mutane 792 da ke damfarar mutane ta hanyar zamba da yaudara ta amfani da hanyoyin sadarwa da kuma yaudara ta hanyar soyayya.
A watan Fabrairu 2025, hukumar EFCC ta shiyyar Legas ta gurfanar da su a gaban kotu bisa tuhuma daban-daban na aikata laifukan damfara da ta’addanci ta internet.
Ƙunshin Ƙarar ta bayyana cewa: "Ku LI Dong da sauran Tara, a watan Disamba, 2024 a Legas, sun haɗa kai domin aikata laifi ta hanyar shiga kwamfutoci da nufin aikata zamba, wanda hakan ya saɓawa Sashe na 27 (1)(b) da kuma ƙarƙashin Sashe na 18(1) na Dokar Laifukan Yanar Gizo ta 2015."
Da farko, waɗanda ake zargin sun musanta laifin amma daga bisani a ranar 5 ga Yuni, 2025 sun amsa laifinsu.
Lauyan masu ƙara, Nnaemeka Omewa, ya roƙi kotu da ta yanke musu hukunci, shi ma lauyan da ke kare su ya goyi baya.
Mai Shari’a Osiagor ya yanke musu hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan gyaran hali, daga ranar da aka kama su, da tarar naira miliyan ɗaya kowannensu.
Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa a mayar da su ƙasarsu ta asali cikin kwana bakwai bayan kammala zaman gidan yari, a bisa umarnin da aka bai wa Shugaban Hukumar Shige da Fice.
Haka kuma, kotun ta bayar da umarnin ƙwace wayoyin hannu, kwamfutoci, da na'urorin sadarwa da aka kama tare da su a yayin samamen da EFCC ta gudanar mai suna “Eagle Flush Operation,” domin mika su ga Gwamnatin Tarayya.