Rasha ta kaddamar da hare-haren jirage marasa matuki 315 da makamai masu linzami 7

Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana cewa Rasha ta kaddamar da jiragen sama marasa matuki guda 315 da makamai masu linzami bakwai cikin dare, yana mai kira ga Amurka da ta yi amfani da ƙarfin ta wajen tilasta wa Rasha zaman lafiya.

Dakarun sojin saman Ukraine sun ce manyan wararen da  hare-haren suka nufa su ne babban birnin ƙasar, Kyiv, inda suka ƙara da cewa sun yi nasarar dakile jirage marasa matuki 284 da kuma dukkan makamai masu linzami.

A birnin da tashar jiragen ruwa na kudu, Odesa, akalla mutane biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wani jirgi mara matuki ya kai, a cewar magajin garin, Gennadiy Trukhanov.

A gefe guda kuwa, hukumomin Rasha sun ce an rufe dukkan filayen jiragen sama da ke biranen Moscow da St Petersburg na ɗan lokaci sakamakon hare-haren jirage marasa matuki daga Ukraine a daren jiya, duk da cewa babu wani rahoton asarar rayuka ko barnar da aka samu.

Previous Post Next Post