Isra’ila Ta Kai Hari Kan Birnin Hodeidah na Yemen, Ta Ce Ana Amfani da Tashar Jiragen Ruwa Don Safarar Makamai

Dakarun Isra’ila sun kaddamar da hare-haren dare kan birnin Hodeidah na kasar Yemen, inda suka ce Houthi na amfani da tashar jiragen ruwa wajen safarar makamai.

Rahotanni daga sojojin Isra’ila da kafafen yada labarai da ke karkashin ikon Houthi sun tabbatar da hare-haren da aka kai a birnin Hodeidah – wata muhimmiya tasha da ake shigowa da kayayyakin agajin jin kai ta ita a kasar Yemen. Wani jami’in Isra’ila ya bayyana yiwuwar daukar matakin killace yankin ta sama da teku idan Houthi suka ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila.

A wata sanarwa daga Houthi bayan harin da aka kai wa filin jirgin saman Sanaa, kungiyar ta ce ba za ta daina goyon bayan Gaza ba, duk da hare-haren Isra’ila.

A yayin da wasu rahotanni ke bayyana cewa an kai harin kan manyan wurare guda biyu a tashar jiragen ruwa, sojojin Isra’ila sun tabbatar da kai harin da jiragen ruwan yaki suka yi da makamai masu linzami, inda suka ce ana amfani da wuraren ne wajen shirya ayyukan soja.

Ba a bayar da rahoton rasa rayuka ko samun raunuka ba daga bangarorin biyu – Isra’ila ko Houthi.

Birnin Hodeidah da ke gabar tekun Red Sea yana da matukar muhimmanci wajen shigowa da kayan abinci da sauran kayayyakin agaji ga al’ummar Yemen da suka tsinci kansu cikin mummunan rikici tun daga 2014.

Isra’ila ta zargi Houthi da amfani da tashar wajen safarar makamai da ta ce ana kai su ga kungiyoyin da Iran ke daukar nauyi. 

A watan Mayu ma, Isra’ila ta kai hari ta sama kan Hodeidah bisa irin wannan zargi.

Kafin harin, dakarun Isra’ila sun fitar da gargadi ga fararen hula su bar tashoshin jiragen ruwa da ke Ras Isa, as-Salif da Hodeidah, da zimmar dakile ayyukan da suke da danganta da Houthi.

Halin da ake ciki yanzu ya kara dagula lamura a yankin, musamman yadda Houthi ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa da ke fuskantar hare-hare a Gaza.

Previous Post Next Post