Wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan ƙungiyar Boko Haram/ISWAP sun sace wani faston Cocin Katolika, Daniel Alfa, tare da wasu mutane tara a kan hanyar Gwoza-Limankara da ke Jihar Borno.
Wani abokin Fasto Alfa a unguwar Pompomari Housing Estate da ke Maiduguri ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata.
A cewarsa, daya daga cikin mutanen da aka kai wa harin ya rasa ransa yayin da yake kokarin tserewa daga hannun ‘yan ta’addan.
Fasto Alfa shi ne shugaban sashen gudanarwa na wata kungiya mai zaman kanta ta kiristoci (NGO). Yana kan hanyarsa ta dawowa daga Mubi tare da wasu ma’aikatan kungiyar guda biyu a cikin mota lokacin da ‘yan ta’addan suka kai musu hari a kan hanyar Gwoza-Limankara.
‘Yan ta’addan sun bindige daya daga cikin ma’aikatan kungiyar har lahira, sannan suka sace Fasto Alfa da dayan abokin aikinsa.
Sauran mutum bakwai da aka sace tare da shi sun hada da wasu da ke tafiya zuwa Gwoza daga bikin aure da suka halarta a yankin Madagali na Jihar Adamawa.