Fiye da Maniyata Miliyan 1.6 Sun Bar Mina Bayan Kammala Manyan Ibadu


Fiye da maniyyata miliyan 1.6 sun ci gaba da jifar shaidan a rana ta uku kuma ta ƙarshe a ranar Lahadi, kafin su wuce zuwa Makkah domin yin Tawaf Al-Wada (Ɗawafin  bankwana).

Daga cikin jimillar maniyyata 1,673,230, kimanin 1,506,576 sun zo daga ƙasashen waje, yayin da 166,654 suka kasance  daga cikin ƙasar ta Saudiyya.

Bayan kammala wannan babban rukuni na Hajj, maniyyata sun fara shirin tafiya zuwa Madinah ko komawa ƙasashensu.

Aikin Hajj 2025 ya ƙare a hukumance a ranar Lahadi, wanda ke nuna ƙarshen zaman maniyyata na kwana biyar a Mina. Yawancin su sun riga sun ziyarci Madinah kafin fara aikin Hajj domin gaisawa ga Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da yin salla a masallacin Masjid-e-Nabawi (SAWW), yayin da wasu suka bar hakan har sai sun kammala dukkan rukunan Hajj.

Yawancin maniyyata sun gaggauta barin Mina kafin faduwar rana domin kaucewa kwana na ƙarin rana wanda zai sa a maimaita jifar. Da yammacin Lahadi, yawancin maniyyatan sun riga sun bar Mina, inda aka ga wuraren da suka cika da jama’a tun ranar Laraba sun koma shiru.

An gudanar da jifar shaidan cikin nasara ba tare da rahoton kowanne hatsari ko cunkoso ba. Don tabbatar da tsaro, hukumomin Saudiyya sun girke kyamarori na tsaro a wuraren Jamarat tare da tura dubban jami’an tsaro don sa ido kan zirga-zirgar maniyyata da amsa musu cikin gaggawa idan an samu matsala.

A wata sanarwa, Mataimakin Sarkin Yankin Makkah, Yarima Saud Bin Mishakk, ya bayyana nasarar kammala Hajj na shekara ta 1446, ba tare da samun wani cikas a bangaren tsaro, lafiya ko  wani abu ba, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito. Haka kuma, ya sanar da fara shirye-shiryen Hajj na shekara ta gaba – 1447 – nan da nan.

A gefe guda kuma, Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta bayyana cewa fiye da ma’aikatan lafiya 5,000 masu aikin sa kai ne suka halarci aikin Hajjin bana domin ƙara inganta hidimar lafiya ga maniyyata.

Wannan yunkuri yana daga cikin shirin sauya fasalin bangaren lafiya da kuma shirin kyautata wa maniyyata, wanda duk su ke daga cikin manyan ginshikan burin Saudi Vision 2030, domin ƙara yawan masu sa kai da ƙarfafa rawar da suke takawa wajen hidimtawa maniyyata.

Previous Post Next Post