Majalisar Ƙasashen Larabawa ta taya Saudiyya murna bisa nasarar gudanar da aikin Hajji

Majalisar Ƙasashen Larabawa ta taya shugabannin Saudiyya da ƙasar murna bisa nasarar da suka samu wajen shiryawa da gudanar da aikin Hajji, inda kusan musulmai miliyan 1.4 suka gudanar da ibada tun daga ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Larabawa, Mohammed Al-Yamahi, ya taya Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman murna bisa nasarar gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuwait (KUNA) ya ruwaito.

Al-Yamahi ya bayyana cewa Saudiyya ta yi amfani da ƙirkirarriyar fasahar zamani  (AI) wajen tafiyar da al’amuran aikin Hajji, wanda ya shafi bayar da abinci, ruwa, matsuguni, sufuri da kuma kula da lafiyar mahajjata a wuraren ibada daban-daban na Makkah da Madinah.

Ya kara da cewa amfani da wadannan sabbin fasahohi da hanyoyin zamani ya taimaka matuka wajen kare lafiya da jin dadin mahajjata, tare da samar da yanayi mai aminci da kwanciyar hankali domin gudanar da ibada cikin sauki.

Al-Yamahi ya bayyana cewa shigar da sabbin fasahohi a wuraren ibadar Musulunci da ke Saudiyya ya kara inganta tsaro, kariya da jin dadin mahajjata, kuma wannan tsari ya zama abin koyi wajen gudanar da daya daga cikin manyan tarukan shekara-shekara a duniya.


Previous Post Next Post