Cristiano Ronaldo Ya Sabunta Kwantiraginsa da Al Nassr Har zuwa 2027

Cristiano Ronaldo ya rattaba hannu kan ƙarin kwantiragi na shekaru biyu da ƙungiyar kwallon ƙafa ta Al Nassr da ke Saudiyya, in ji wata sanarwar da ƙungiyar ta fitar ranar Alhamis, bayan makonni da dama ana jita-jitar ƙungiyar da zai koma a kakar wasa mai zuwa.



ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X cewa “Cristiano Ronaldo zai cigaba da zama a @AlNassrFC har zuwa 2027,”.

Kafin sanarwar a hukuma, Al Nassr ta saki wani bidiyo mai ɗaukar hankali, inda aka ga Ronaldo mai shekaru 40 yana tafiya a gefen rairayin bakin teku yana cewa: “Al Nassr forever.”

Fitaccen ɗan wasan Portugal ya koma Al Nassr a shekarar 2023, matakin da ya haifar da shigar fitattun 'yan wasa da dama ƙasar Saudiyya, musamman masu gab da ajiye takalman kwallo.

A watan da ya gabata, Ronaldo ya sanya wani rubutu da ke cewa “This chapter is over” a shafinsa na sada zumunta, sa’o’i bayan ƙarewar gasar Saudi Pro League inda Al Nassr ta kammala a matsayi na uku ba tare da lashe ko da kofi ɗaya ba.

Wata majiya daga Public Investment Fund  (PIF), wanda ke da hannun jari a ƙwallon ƙafa ta Saudiyya, ya shaida wa AFP cewa: “Zamansa (Ronaldo) na taka rawa wajen haɓaka gasar Saudiyya a cikin shekaru biyu da rabi da suka wuce. Ya buɗe ƙofa ga manyan ’yan wasa da matasa su shigo Saudiyya.”

PIF, wanda ke da alaƙa da manyan masu saka hannun jari a Saudiyya, na da iko da wasu ƙungiyoyi a Pro League, ciki har da Al Nassr, Al Hilal da Al Ahli.

Previous Post Next Post