PDP a Jigawa Ta Shirya Shiga Haɗakar Hamayya Ta ADA, Inda Ta Kafa Kwamitoci a Matakai Daban-daban

Jam’iyyar PDP a jihar Jigawa ta kafa kwamitin gudanarwa na jiha da na kananan hukumomi domin shirye-shiryen shiga gungun hadakar siyasa mai suna All Democratic Alliance (ADA).



Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Jiha, Aminu Abdullahi Taura, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kaddamar da kwamitocin 27 na kananan hukumomi a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce PDP a jihar Jigawa na shirin hada kai da sabuwar tafiyar siyasa domin neman karbe mulki daga hannun jam’iyyar APC a zaben 2027 mai zuwa.

Taura ya bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da shawarwari da masu da tsaki da manyan ’yan siyasa da shugabanni a fadin jihar, domin ganin an kifar da jam’iyya mai mulki a matakin jiha da na kasa.

A cewarsa: “Mun tattauna kuma muka kaddamar da kwamitin jiha domin kula da aiwatar da wannan tsari. Haka nan mun kafa kwamitoci iri ɗaya a dukkan kananan hukumomi.”

Ya ƙara da cewa: “Kwamitocin kananan hukumomi za su yi har zuwa matakin gundumomi da rumfunan zaɓe domin tabbatar da daidaiton tsarin daga tushe.”

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce zai shiga cikin kowace irin hadaka da za ta kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar APC.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa karkashin jagorancin Sule Lamido, jam’iyyar na ci gaba da shirye-shiryen shiga tsarin ADA domin tsara dabarun fitar da APC daga mulki.

Ya kuma bukaci ’yan jam’iyyar da su kasance masu haɗin kai, tare da jiran umarni na gaba daga shugabanni.

Previous Post Next Post