Kylian Mbappe Ya Maka Kungiyar Kwallon Kafa Ta PSG a Kotu

Ɗan wasan gaba a Real Madrid, Kylian Mbappe, ya shigar da ƙara a gaban kotu kan tsohuwar ƙungiyarsa, Paris Saint-Germain (PSG), bisa zargin yunƙurin tilasta masa sabunta kwantiragi da kuma tsangwamarsa ta hanyar hana shi atisaye tare da abokan wasansa a shekarar 2023.



Jaridar Le Parisien ta ruwaito cewa an bude binciken shari’ar Mbappe, wanda ke matsayin kyaftin din ƙasar Faransa, ya shigar da ƙara a ranar 16 ga Mayu bisa zargin “cin zarafi ta hanyar matsin lamba da ya cutar da shi.”

Ƙarar ta shafi yadda PSG ta mu'amalanci Mbappe a kakar bazarar shekarar 2023, lokacin da aka ware shi daga tawagar farko saboda kin sabunta kwantiragin sa da kungiyar.

Rahotanni sun ce an riga an nada alkalai guda biyu da za su jagoranci shari'ar, da aka fara gudanar da ita a hukumance ranar Talata.

Mbappe ya bar PSG  zuwa Real Madrid a karshen kwantiraginsa, kuma ya fara nuna bajinta tun shiga sabuwar ƙungiyarsa, inda tauraruwarsa ke haskakawa.

Wannan mataki na shigar da ƙara na iya haifar da sabuwar rashin jituwa tsakanin ɗan wasan da tsohuwar ƙungiyarsa, wadda ke fuskantar suka kan yadda take mu’amala da ’yan wasanta, musamman a lokutan sabunta kwantiragi.

Previous Post Next Post