'Yan Bindiga Sun Yiwa Sojoji Kwantan Bauna a Neja

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da harin kwantan bauna da wasu 'yan bindiga suka kai wa barikin soji da ke karamar hukumar Mariga a jihar Neja, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu sojoji.


A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Laraba, rundunar ta bayyana cewa dakarunta na kasa da na  sama sun “halaka” dimbin 'yan bindigar da suka kai harin.

A cewar sojin, harin ya kasance a wurare guda uku, inda suka kai farmaki a Barikin soji na Kwanar Dutse da Mairiga da ke jihar Neja, da kuma Anguwan Turai da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna,  dukkannin hare-haren an kai su ne a ranar 24 ga Yuni, 2025.

Rundunar ba ta fadi adadin sojojin da suka rasa rayukansu ba, amma ta tabbatar da cewa wasu “gwarazan dakarunta sun sadaukar da rayukansu wajen kare ƙasar nan,” yayin da wasu sojoji guda hudu suka jikkata, yanzu haka suna samun kulawa a asibiti.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa akalla sojoji 20 ne suka mutu a harin da aka kai barikin sojin da ke Kwanar Dutse, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kakakin rundunar soji, Onyechi Anele, ta bayyana cewa za ta yi karin bayani daga baya, yayin da kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Neja.

Harin ya zo ne a dai-dai lokacin da wasu 'yan bindiga suka kashe mutane kimanin 15 a kauyen Tofa da ke gundumar Magami a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.

A dai wannan rana, an yi wata arangama tsakanin dakarun tsaro da gungun mayakan  Bello Turji a kusa da kauyen Cida da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Sakkwato, inda rahotanni suka ce fiye da mutum 100 ne suka rasa rayukansu.

Har yanzu rundunar sojin ba ta fitar da wata sanarwa dangane da hare-haren da suka auku a Zamfara da Sakkwato ba.

Previous Post Next Post