Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Ali Bukar Dalori, ya isa babban tarayya Abuja domin fara gudanar da aikinsa.
Dalori ya hau kujerar shugabancin APC a matsayin mukaddashi bayan murabus din da Abdullahi Ganduje ya yi a ranar Juma’a.
Ganduje ya bayyana matsalolin lafiya a matsayin dalilin da ya sa ya ajiye mukamin.
Sai dai ana ta rade-radin cewa an tilasta masa barin ofishin ne.
Kafin hawa matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Dalori shi ne Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Arewa.
Dan siyasar ya fito ne daga jihar Borno, da ke yankin Arewa maso Gabas.
Tags:
Siyasa