Kungiyar kwallon kafa ta AS Monaco ta sanar da daukar ɗan wasan tsakiya, Paul Pogba, kan kwantiragi shekaru biyu.
Pogba zai fara sabuwar rayuwa ta kwallo a kasar haihuwarsa bayan shafe wani lokaci yana fuskantar hukuncin dakatarwa saboda shan maganin kara kuzari da aka haramta.
Tsohon ɗan wasan Manchester United ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyu da kungiyar ta Monaco.
A wata sanarwa da Monaco ta fitar ta ce: “AS Monaco na farin cikin sanar da isowar Paul Pogba. Zakaran Duniya na Faransa ya sanya hannu kan yarjejeniya ta tsawon kakar wasanni biyu, kuma zai kasance a kungiyar har zuwa 30 ga watan Yuni, 2027.”
Pogba ya koma kungiyar ta Ligue 1 bayan Juventus ta soke kwangilarsa a watan Nuwamba na shekarar 2024, sakamakon gwajin da ya nuna yana shan kwayar dehydroepiandrosterone (DHEA).
An yankewa ɗan wasan mai shekaru 32 hukuncin dakatarwa na shekaru hudu, kafin daga bisani aka rage zuwa wata 18.
