’Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin ’Yan Sanda a Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari kan wasu ’yan sandan da ke sintiri a kauyen Makuku, da ke cikin karamar hukumar Sakaba.



Daraktan dake kula da harkokin tsaro a ofishin gwamna, Malam Abdulrahman Zagga, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Bagudo ranar Asabar.

Zagga ya ce maharan sun yi awon gaba da wasu bindigogi, da bai bayyana adadinsu ba, tare da cinna wuta a motar sintiri kirar Toyota Hilux. Ya bayyana cewa shingen da aka kai wa harin na wucin gadi ne, ba cikakken ofishin ’yan sanda ba, kuma babu asarar rai da aka samu.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tafi da wasu shanu da ake zargin sun sato su ne daga Jihar Neja, kuma suna kan hanyar su ne na  ketarawa  Zamfara.

Biyo bayan lamarin, gwamnatin jihar ta nemi taimakon rundunar sojin saman. 

Rahotanni sun bayyana cewa jiragen yaki sojojin sun gudanar da luguden wutakan 'yan ta'addan wanda ya taimaka wajen tarwatsa su.

Malam Zagga ya jaddada cewa gwamnatin Kebbi bata yi wata yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin ’yan bindiga ba, inda ya bayyana masu ba da bayanai ga maharan a matsayin babbar barazana ga kokarin da gwamnati ke yi wajen tabbatar da tsaro.

Ya kuma kara da cewa irin wadannan hare-hare kan karu ne a lokacin damina saboda ’yan bindiga na amfani da damar tilasta wa manoma da al’ummomin karkara biyan kudaden haraji da na fansa.

Previous Post Next Post