Tsohon shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano SEMA Kuma sarkin fadar Karaye, Comrade Sale Aliyu Jili, ya ce samar da haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki a hankar iftila'i, ne zai kawo ƙarshen matsalar ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu jahohi.
A zantawarsa da KRM Hausa, Comrade Jili, ya ce kafa kwamitoci na bada agajin gaggawa a Kananan hukumomi da suka yi a baya, ya taimaka ta hanyar wayar da kan al'umma musamman a Karkara, wanda hakan yayi tasiri sosai wajen nunawa al'umma illolin ambaliyar ruwa da sauransu.
Kazalika Jili, ya shawarci gwamnatin Jihar Kano kan ta karkade dokar da hukumar ta SEMA ta samar a baya domin aiwatar da ita, wanda yin hakan zai taimakawa hukumar don samu damar yin ayyukan agaji a koda yaushe.
Daga nan sai ya shawarci masu yin gine-gine akan hanyoyin ruwa da masu yin gini cikin gaggawa dasu kaucewa wannan dabi'ar domin tana daga cikin matsalolin dake haddasa rushewar gidaje a lokutan damina.