INEC Ta Fara Aiwatar Da Bukatar Yiwa Sabbin Jam'iyyu Rigista Ciki Har Da ADA

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta fara aiwatar da bukatar rajistar sabbin jam’iyyu da suka hada da All Democratic Alliance (ADA).

Wannan mataki na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan hukumar ta bayyana cewa Jam'iyyar ADA, da wasu jiga-jigan ‘yan adawa suka kirkiro, ba ta cika sharuddan rajista ba tukuna.



A wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya fitar a ranar Laraba, ya ce ADA na cikin jam’iyyu 110 da ake duba yiwuwar musu rajistarsu a halin yanzu.

Sashe na sanarwar ya ce:

A ranar Litinin, 23 ga Yuni 2025, hukumar ta karɓi takardun neman bukatar yin  rajista daga kungiyoyi 110 da ke sha’awar zama jam’iyyun siyasa. kuma Muna ci gaba da tantance bukatun wadannan kungiyoyi da muka karɓa bisa tsarin da doka da ka'idojinmu suka tanada.

Yakubu ya ce ''mun tabbatar da karɓar dukkan bukatun da aka aiko mana, banda guda shida da aka kawo a baya bayan nan, wanda za mu tabbatar kafin ƙarshen mako.”

Farfesa Yakubu ya kuma ja hankalin ‘yan Najeriya da ke da niyyar kafa sabbin jam’iyyu da su duba manhajar da ke dauke da ka’idoji da dokokin rajistar jam’iyyu na 2022, wadda tuni aka saka a shafin yanar gizon INEC.

Ana sa ran matakin zai bude sabon shafi a siyasar Najeriya, musamman ganin yanda wasu tsofaffin shugabanni ke hada kai don kafa sabbin jam’iyyu.

Previous Post Next Post