Del Piero Ya Yi Hasashen Real Madrid Za Ta Doke Juventus a Gasar FIFA Club World Cup

Tsohon dan wasan Italiya, Alessandro Del Piero, ya yi hasashen cewa kungiyar Real Madrid za ta doke Juventus a gasar FIFA Club World Cup da ke gudana a Amurka.



A ranar Talata ne Real Madrid za ta kara da Juventus a zagaye na 16 na gasar, inda duk wanda ya yi nasara zai samu damar tsallakewa zuwa matakin daf da na kusa da karshe.

Del Piero,  ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a tashar ANTV, kamar yadda shafin JuventusNews24 ya ruwaito, ya ce duk da cewa zuciyarsa tana tare da tsohuwar kungiyarsa Juventus, yana ganin Real Madrid za ta yi nasara a wasan.

A cewarsa: “ Kamar yadda kuka sani zuciyata ba ta rabuwa da launin fari da baki (Juventus), kuma hakan ba zai canza ba,” in ji Del Piero. “Don haka ina fatan hasashen nawa ya zama kuskure, amma ina ganin Real Madrid za ta yi nasara.”

Ana sa ran take wasan  da karfe 9 na dare agogon Najeriya.

Previous Post Next Post