Rundunar sojin Brigade na 1 ta Najeriya ta samu nasarar kashe wani babban shugaban ’yan ta’adda da aka bayyana da suna Mai Dada, a wani samamen mayar da martani da aka gudanar a karamar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Wata majiyar da ke da masaniya da yadda aikin samamen ya gudana ta shaida wa Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN) cewa an cafke wasu mutune da dama da ake zargi da taimawa ta'addaci a yayin aikin samamen da aka gudanar daga 25 zuwa 26 ga watan Yuni.
A Jihar Kaduna kuwa, majiyar ta ce sojojin bataliya ta 2 da ke aikin sintiri a Birnin Gwari sun yi arangama da wasu ’yan bindiga da ke kan babur, inda suka y nasarar kwato bindiga kirar AK-47 dauke da harsasai 30 na 7.62mm.
Majiyar ta kara da cewa a fadin kasar nan, sojoji sun cafke wasu da dama da ake zargi da aikata vlaifuka daban-daban tare da kwato makamai da alburusai fiye da 1,000 a jerin ayyukan da suka gudanar.
A yankin Arewa Maso Gabas, majiyar ta bayyana cewa dakarun runduna ta 82 Task Force Battalion, yayin sintiri a Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza ta Jihar Borno, sun gano harsasai 408 na 12.7mm, da wasu harsasai 1,200 na 7.62mm, da RPG 40mm guda biyu, a hanyar da mayakan ISWAP/JAS kan bi.
Kazalika, sojojin 21 Special Armoured Brigade sun kashe ’yan ta’adda uku a wani sumame da suka kai a karamar hukumar Bama, inda suka kwato bindigar gargajiya sannan suka lalata kayayyakin ’yan ta’addan.
A Monguno, an cafke wani mutum da ake zargi da hannu bayan da sojoji suka kama wata mota dauke da kayan da ake zargin na ’yan ta’adda ne.
Bincike ya gano kayan da aka kwato sun hada da: lita 65 na man fetur (PMS), buhuna hudu na shinkafa, buhuna biyar na gyada, buhuna hudu na takin NPK, doya, fitilu na babur guda bakwai, fitilu masu amfani da hasken rana guda 10, buhuna 2,000, fanel na hasken rana guda hudu da wayar hannu daya.
A Jihar Filato, majiyar ta ce sojojin Operation Safe Haven sun gudanar da farmaki a kauyuka Tangur, Kwakas, Horop, Tulus, Jinak, da Hokk a karamar hukumar Bokkos. An ce sojoji sun yi amfani da jirgin leken asiri na drone wajen zakulo maboyar bata-garin, inda suka kwato bindiga da aka yar bayan ganin sojojin.
A Benue kuwa, sojojin Operation Whirl Stroke sun kubutar da fasinjoji biyar tare da kwato wata mota a kan hanyar Peykia zuwa Wukari da ke cikin karamar hukumar Ukum.