Dakarun sojin Isra’ila sun kashe aƙalla Falasdinawa 27 tare da jikkata wasu 90 yayin da suka bude wuta a kusa da wata cibiyar raba kayayyakin agaji da ke Rafah, a cewar Ma’aikatar Lafiya ta Gaza.
Kisan ya faru ne da safiyar Talata a wurin da ake kira Flag Roundabout, kusa da cibiyar bada agaji ta Gaza Humanitarian Foundation (GHF). Wannan ne karo na uku da ake kai irin wannan hari a cikin kwanaki uku a kusa da wannan cibiyar bayar da kayayyakin agaji da ke Rafah.
Hukumomin Gaza sun ce sama da mutane 100 da ke neman agaji aka kashe tun bayan da da Amurka da Isra’ila suka amince GHF ta fara aiki a zirin Gaza tun daga 27 ga Mayu, inda ake samun rahotannin tashin hankali da rudani sosai a wuraren rabon kayan agaji.
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa ta harba bindiga ne bayan wasu mutane suka kauce daga hanyoyin da aka kayyade zuwa cibiyar raba kayan agajin.
Ta ce waɗannan mutane sun kai kimanin mita 500 daga cibiyar,
Ana DAI gudanar da bincike kan rahoton asarar rayuka.
Shugaban sashen kididdiga na Ma’aikatar Lafiyar Gaza, Zaher al-Waheidi, ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu.
Hisham Mhanna, mai magana da yawun Hukumar Red Cross ta Duniya, ya ce an kawo mutane 184 da suka jikkata zuwa asibitin don neman agajin gaggawa a asibiti da ke Rafah, inda aka iske 19 daga cikinsu sun riga mu gidan gaskiya, sannan wasu 8 suka mutu daga bisani sakamakon raunuka.
Gwamnatin Gaza ta zargi Isra’ila da aikata "mummunan kisan kiyashi da ake maimaitawa da gangan", inda ta ce ana azabtar da Falasdinawa da ke jin yunwa a hanyar su ta zuwa cibiyoyin GHF
Kiran gudanar da bincike
Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ta bukaci gudanar da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan yawan harbin jama’ar da ke neman abinci a Gaza.
“Ba abin da za a amince bane a dinga sa rayuwar Falasdinawa cikin hadari ba, don neman abinci,” in ji Sakatare Majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres.
Ya kara da cewa “Ina kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa kuma a hukunta wadanda suka aikata hakan.”
Wata mace mai suna Rasha al-Nahal ta shaida wa kamfanin labarai na Associated Press cewa “an harba bindiga kan mai uwa da wabi,” inda ta ga mutane fiye da goma sha biyu sun mutu, wasu da dama kuma sun jikkata.
Ta ce da ta isa wurin rabon agaji, basu samu komai ba, sannan sojojin Isra’ila sun sake bude musu wuta yayin da suke komawa.
Wata mashaidar gani da ido daga Khan Younis mai suna Neima al-Aaraj, ta ce harin da aka kai "kan kowa” aka yi shi.
Rundunar sojin Isra’ila a cikin sanarwarta ta ce ta fara da harbin gargadi ne, kuma bayan da “masu nuna amincewa” suka ki janyewa, an harba kusa da su. Ta musanta cewa ta bude wuta kai tsaye kan fararen hula ko ta hana su samun kayayyakin agaji.
Wannan bayani na sojojin Isra’ila dai yana da kamanceceniya da na hare-haren da suka gabata a ranar Lahadi (inda aka kashe mutane 31) da na Litinin (inda aka kashe mutane 3).