Jamie Gittens Ya Koma Chelsea Daga Borussia Dortmund

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta kammala yarjejeniya domin daukar dan wasan gaba, Jamie Gittens, daga Borussia Dortmund.

Kungiyoyin biyu sun dade suna tattaunawa kan Ɗan wasan, yayin da suke fafatawa a gasar Club World Cup ta 2025 a kasar Amurka.



Duk da cewa Bayern Munich ma na zawarcin ɗan wasan, Chelsea ta yi nasarar cimma matsaya da Dortmund domin daukar Gittens.

Ɗan wasan mai shekaru 20 zai koma filin Stamford Bridge inda ake sa ran zai rattaba hannu kan kwangila ta dogon lokaci.

A farkon wannan watan, Dortmund ta ki amincewa da tayin fam miliyan £42 da Chelsea ta yi, wanda hakan ya sa ba a kammala cinikin ba, kafin sake bude damar daukar 'yan wasa.

A kakar da ta gabata, Gittens ya zura kwallaye 12 tare da taimakawa aka zura guda 5 a wasanni 48 da ya buga a gasar.

Tun a baya dai Gittens ya taba zama dan wasan makarantar kwallon kafa ta Chelsea kafin daga bisani ya samu damar zuwa Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City.

Previous Post Next Post