EFCC Na Neman Wasu Mutum Biyu Bisa Zargin Damfara a Crypto

EFCC ta sanar da cewa tana neman wasu mutane biyu ruwa a jallo bisa zarginsu da aikata damfara a kasuwar hada-hadar kudi ta Crypto Bridge (CBEX).

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na sada zumunta a ranar Laraba, ta bayyana sunayen wadanda ake zargin da laifin da suka aikata. Wadanda ake zargin su ne Folashade Odelana, mai shekaru 31, da kuma Bamidele Ayodele Abiodun, mai shekaru 32.

EFCC ta ce mutanen biyun na fuskantar zargi ne kan laifin kulla makirci da aikata zamba, wanda ya haddasa asara mai yawan gaske ga masu saka jari a kasuwar CBEX.

“Wannan aiki na damfara ya shafi daruruwan mutane da suka saka jari a kasuwar Crypto Bridge tare da fatan samun riba, amma suka gamu da asara sakamakon ayyukan wadannan da ake zargi,” in ji sanarwar.

Hukumar ta bukaci duk wanda ke da masaniya game da inda mutanen suke ko wani bayani da zai iya taimakawa wajen kamasu, da ya tuntubi ofishin EFCC mafi kusa ko kuma ya kira layukan da hukumar ta sanya.

Previous Post Next Post