Rundunar ‘Yan Sanda a Plateau Ta Ƙarfafa Tsaro Gabanin Bikin Sallah

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Plateau ta bayyana cewa ta ɗauki kwararan matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar da bikin Sallah babba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar, CP Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya mika sakon fatan alheri ga daukacin Musulman  jihar, yana mai bukatar su yi biki cikin kwanciyar hankali da bin doka.

A cewarsa, rundunar ta kammala shirin tabbatar da tsaro ta hanyar tura jami’ai zuwa dukkan sassan birnin Jos-Bukuru da kuma kananan hukumomi 17 na jihar. Bugu da ƙari, an ware jami’ai domin tsare masallatai, filayen idi, wuraren shakatawa da sauran wuraren da ake sa ran tarukan jama’a. Rundunar ta kuma tura jami’an leƙen asiri domin tattara bayanai da gano duk wani barazana.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye, shugabannin al’umma, da na addini da su taimaka wajen wayar da kan matasa da mabiyansu kan muhimmancin zaman lafiya da haɗin kai a lokacin bikin. Haka zalika, ya bukaci al’umma su kai rahoto ga hukumomin tsaro idan sun ga wani abu da ke ɗaukar hankali ko wanda ke barazana ga zaman lafiya.

Rundunar ta kuma sanar da dokar hana zirga-zirgar Keke Napep a ranar Sallah, inda aka jaddada cewa haramcin babura a cikin Jos-Bukuru da yankunan da ke cikin tsarin birnin Jos na nan daram. Rundunar ta gargadi masu karya wannan doka da cewa za su fuskanci hukunci.

A ƙarshe, CP Adesina ya ja kunnen duk masu niyyar tayar da zaune tsaye ko tada fitina da su yi hattara, domin rundunar tana da cikakken shiri da kayan aiki na fuskantar duk wani kalubale.

Previous Post Next Post