Rundunar 'Yan Sanda ta Jihar Kano na sanar da ci gaban da aka samu a bincike kan lamarin da ya haddasa kisan gilla ga CSP Baba Ali, wanda shi ne Divisional Police Officer (DPO) na karamar hukumar Rano, da kuma lalata dukiyoyi a lokacin da lamarin ya faru.
Bayan kammala bincike mai zurfi, rundunar ta gurfanar da mutum 29 a gaban Kotun Majistare mai lamba 20 da ke Nomansland, Kano, bisa zarge-zarge da suka shafi wannan mummunan lamari.
Mutum 14 daga cikin wadanda aka kama, ana zarginsu da aikata laifuka kamar haka:
-
Hadin baki wajen aikata laifi
-
Tunzura jama'a
-
Kona dukiya da gangan
-
Taɓa kadarar wasu
-
Jikkata mutane da gangan
-
Sata
Sunayen wadanda ake zargin sune kamar haka:
-
Bala Yusuf
-
Bala Mohammed
-
Abdulrashid Ibrahim
-
Abdullahi Salisu Kere
-
Sadiq Buhari
-
Yunusa Adamu
-
Musa Minkaila
-
Mamuda Mohammed
-
Ismail Mamuda
-
Usman Shu'aibu
-
Musa Hassan Black
-
Abdulrashid Munkail
-
Umar Ado Nadada
-
Sabitu Abubakar
Dukkansu sun fito nedaga karamar hukumar Rano, Jihar Kano.
Sauran mutum 15 kuma ana zarginsu da:
-
Hadin baki wajen aikata laifi
-
Tunzura jama'a
-
Lalata dukiya
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa za a tabbatar da adalci a wannan lamari, tana mai bayyana godiyarta ga jama’a bisa ta’aziyya, addu’o’i, goyon baya da fahimta da suka nuna yayin gudanar da bincike.
A karshe, rundunar na kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa daukar doka a hannunsu.
Rundunar za ta ci gaba da tabbatar da doka da oda da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar