Elon Musk Ya Bayyana Nadama Kan Zagin Trump a Kafafen Sada Zumunta.

Elon Musk, wanda ya shahara a fannin fasaha kuma  attajiri,  ya bayyana cewa yana nadamar yadda ya soki Shugaban Amurka Donald Trump a kafafen sada zumunta, bayan wani sabani mai zafi da ta faru a bainar jama'a tsakaninsu.

A wani rubutu da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta mai suna X a safiyar Laraba, Musk ya ce:

“Ina nadamar wasu daga cikin sakonnin da na wallafa game da Shugaba Donald Trump a makon da ya gabata. Sun yi kaushi fiye da kima.”

Musk bai bayyana ainihin wanne sako ko zargi ya fi nadama akansa ba. Sai dai wannan bayani nasa na nadama ya zo ne bayan da ya rika caccakar Trump da wasu kalamai masu zafi, ciki har da zargin da yayi wanda ba shi da hujja na cewa gwamnatin Trump ta ki sako wasu bayanai game da Jeffrey Epstein, don kare shugaban daga haduwa da marigayin mai kudi wanda aka yanke masa hukunci kan laifukan lalata.

Tun da fari,  Musk yana daya daga cikin masu goyon bayan Trump a lokacin yakin neman zabensa da kuma a farkon wa'adinsa. 

Amma a  makon da ya gabata, ya bayyana kin amincewarsa da sabon kudirin da Trump ya gabatar na  haraji da karin kashe kudade, wanda ya kira da  “ abin kunya”.

Musk ya ci gaba da suka tsagwaronta a kan Trump da tsare-tsaren kashe kudi na jam’iyyar Republican, abin da ya haifar da wani rikici mai tsanani tsakanin su biyu, dukkanin su  manyan mutane a duniya.

Previous Post Next Post