Yawan Falasdinawa Da Suka Mutu A Yakin Isra'ila da Hamas Ya Haura 55,000

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana a ranar Laraba cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu tun bayan fara yakin da aka kwashe watanni 20 tsakanin Isra’ila da Hamas ya haura 55,000.

Wannan adadi bai bambanta tsakanin fararen hula da mayaƙa ba, sai dai ma’aikatar ta ce Mata da Yara ne suka fi yawa cikin wannan adadin.

Yakin wanda ya fara  bayan hare-haren da Hamas ta kai kudancin Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023, ya ci gaba da yin barna ba tare da alamun kawo karshen shi ba. 

Isra’ila na cewa ta na kai hare-hare ne kan mayaka kawai, tana zargin Hamas da fakewa da fararen hula saboda yadda suke gudanar da ayyukansu a cikin yankunan da ke cike da mutane.

Rahoton ya ce mutane 55,104 ne suka mutu tun bayan fara yakin, kuma 127,394 ne suka jikkata. Akwai kuma yuwuwar cewa za a iya samun daruruwan gawarwaki a  karkashin gine-ginen da suka rushe ko a wuraren da ba a iya shiga saboda matsalar rashin tsaro.

Sojojin Isra’ila sun lalata gagarumin yankin Gaza, inda aka tilastawa fiye da kashi 90 cikin 100 na al’ummar yankin barin gidajensu. 

A makonnin baya-bayan nan, Isra’ila ta maida fiye da rabin yankin gabar tekun Gaza zuwa wani yankin soja, ciki har da birnin Rafah da yanzu ba kowa a ciki.

Yaki ya sake dawowa Gaza bayan Isra’ila ta kawo karshen yarjejeniyar zaman lafiya da Hamas, inda ta kaddamar da takunkumi na tsawon wata biyu da rabi. Wannan ya haifar da fargabar yunwa, kuma ko da yake an ɗan sassauta takunkumin a watan Mayu, shirin bayar da agajin da Isra’ila da Amurka ke marawa baya ya gamu da cikas sakamakon rikici da tashin hankali. 

Majalisar Dinkin Duniya na cewa tana fuskantar kalubale wajen shigar da kayan abinci saboda takunkumin Isra’ila, tabarbarewar doka da oda, da sace-sacen kayan agaji.

Isra’ila na zargin Hamas da karkatar da kayayyakin agajin don amfani da shi wajen yakin, amma MDD da kungiyoyin bada agaji sun musanta hakan, suna cewa babu wata shaida da ke nuna hakan yana faruwa.

Ko da Hamas na fuskantar manyan asara ta bangaren soja, Isra’ila ta bayyana cewa ta kashe mayakan Hamas fiye da 20,000, duk da cewa ba ta fitar da hujjoji ba. Har ya zuwa yanzu, mayakan na riƙe da fursunoni 55,  ƙasa da rabinsu ne ake kyautata zaton suna raye. Hamas na ci gaba da rike wasu yankuna da ba sa karkashin ikon sojoji, duk da cewa an sha yin zanga-zanga a kan ta a bana.

Previous Post Next Post