Yan Sanda a Adamawa Sun Kama Matasa Bakwai da Ake Zargi da Fashi da Makami

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta cafke matasa bakwai da ake zargi da shiga cikin wani rukuni na masu aikata laifuka da ake kira ‘Shila Boys’, wadanda ake zargi da fashi da makami.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa an kama matasan ne a yayin da suka je yin  fashi a unguwar Federal Housing Estate da ke Bajabure, karamar hukumar Girei.



An bayyana cewa an kama su ne a ranar 9 ga Yuni, 2025, bayan samun kiran gaggawa.

Sunayen wadanda aka kama sun hada da:

Ja’afar Umar, mai shekara 16

Bulama Abba, shekara 15

Dalha Mohammed, shekara 16

Saidu Abba, shekara 18

Safiyanu Yunusa, shekara 15

Mohammed Abubakar, shekara 15

Abba Ibrahim, shekara 15

Dukkansu mazauna unguwar Jambutu ce a karamar hukumar Yola ta Arewa.

A cewar SP Nguroje, an kwato naira 12,350, wuka guda daya, da wayoyi biyu daga hannun wadanda ake zargin, kuma ana amfani da su a matsayin kayan shaidar bincike.

“Wadannan Matasan sun kaiwa al'umma hari inda suka kwace musu dukiyoyinsu, suna amfani da makamai da ke haddasa tsoro da firgici,” in ji Nguroje.

Ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO na Viniklang sun yi hanzarin zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka cafke su nan take.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarni cewa a gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Previous Post Next Post