Sojojin Isra’ila kaɗai nake gani da Makamai a Gaza.

 Wata likitar tiyata daga Birtaniya da ta yi aiki a Gaza, Dr. Victoria Rose, ta bayyana cewa a duk lokacin da ta ke aiki a yankin, ba ta taɓa ganin wani ɗan Gaza dauke da makami ko kayan soja ba — sai dai kawai sojojin Isra’ila.

Dr. Rose ta shaida wa Sky News cewa,  an samu matuƙar ƙara yawan hare-haren bama-bamai a Gaza, wanda ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

"Ana samun  ƙaruwa munanan hare-haren bama-bamai, wanda ya saka mutane cikin halin tashin hankali,” in ji ta.

Asibitoci na cikin hatsari duk da kariyar dokar duniya.

Tun bayan fara yakin a watan Oktoba 2023, an rika kai hare-hare kan asibitocin Gaza — duk da cewa doka ta kasa da kasa na ba su kariya.

Rundunar sojojin Isra’ila (IDF) na zargin cewa kungiyar Hamas na amfani da asibitoci a matsayin sansanoni ko mafaka. Sai dai Dr. Rose — wacce likitar tiyata ce a asusun kiwon lafiyar Birtaniya (NHS) — ta ce babu wata hujja da ta gani da ke tabbatar da hakan.

“Ban taɓa gani ko yi wa wani jinya a cikin asibitocin da na yi aiki da ke sanye da kayan soja ko dauke da makami ba. 

Waɗanda na ke gani kaɗai Su kaɗai  a Gaza da kayan Soja su ne sojojin IDF,” in ji ta, ta cikin wata hira da aka yi da ita a shirin Sunday Morning with Trevor Phillips.

Likitocin Gaza na Fuskantar wahalhalu da Fargaba

Dr. Rose ta ce wannan yaki na da mummunan tasiri ga likitoci da sauran ma’aikatan jinya a Gaza. Wasu daga cikin abokan aikinta na Falasdinu sun bayyana cewa sun fi so su mutu fiye da ci gaba da jure wannan hali.

“Wasu abokan aikina sun ce su fi so su mutu  fiye da ci gaba da rayuwa a cikin wannan yakin,” in ji ta.

Matsalar abinci da kiwon Lafiya na kara ta'azzara

Ta ce halin kiwon lafiya a Gaza na kara tabarbarewa sakamakon matsananciyar matsalar rashin abinci da kuma hana kai kayayyakin agaji da dakarun Isra’ila ke yi na tsawon watanni.

“Karancin abinci matsala ce mai tsanani a Gaza, musamman ga yara ƙanana,” in ji ta.

Ta kara da cewa lokacin da take can, yawan yaduwar cututtuka na ƙaruwa.

“Mun rika ganin yara da yawa na mutuwa da cutar sepsis — cutar da za a iya magancewa da sauƙi a kasashen yamma,” in ji ta.

Previous Post Next Post