Fiye da Mutane 40 Sun Rasu a Wani Hari Da Aka Kai Asibiti a Sudan — WHO

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce fiye da mutane 40, ciki har da kananan yara da ma’aikatan lafiya, sun mutu a wani mummunan hari da aka kai wani asibitin kasar Sudan a karshen mako.


Shugaban WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ne ya bayyana hakan  ranar Talata, yana mai cewa harin ya auku ne a Asibitin Al Mujlad da ke yankin Kordofan ta Yamma, kusa da inda ake fafatawa tsakanin dakarun sojin Sudan da rundunar ‘yan tawaye ta Rapid Support Forces (RSF).

Duk da cewa bai bayyana waɗanda suka kai harin ba, Dr. Tedros ya yi kira da a daina kai hare-hare kan cibiyoyin lafiya, yana mai jaddada muhimmancin kare rayukan ma’aikatan lafiya da marasa lafiya a lokacin rikici.

Al Mujlad na daga cikin yankunan da ke fama da rikice-rikicen soja, tun bayan barkewar yaki tsakanin sojojin gwamnati da RSF a shekara ta 2023, wanda ya jefa kasar cikin halin tashin hankali da neman bukatar jin kai sosai.

Previous Post Next Post