'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Jihar Neja, Sun Yi Gaba da Mutane Bakwai da Babura Biyar

 Akalla mutum bakwai ne aka sace a wani sabon hari da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a garin Hayin-Gando da ke Jihar Neja a ranar 22 ga watan Yuni.

Wani mai bincike kan lamuran tsaro, Zagazola Makama,  ya ce wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa harin wani bangare ne na ci gaba da farmakin da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke kaiwa a yankin.

Wadanda aka sace sun hada da:

  • Sani Mohammed

  • Yahaya Sani

  • Ibrahim Harka

  • Naraki Habu

  • Zargali Auwal

  • Auwal Gandu

  • Musbahu Ruwa

Dukkansu maza ne daga kauyen Hayin-Gando.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kwace babura guda biyar, mallakin wadanda aka sace.

Dakarun sojin tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun fara sintiri a yankin domin ceto wadanda aka sace da kuma tabbatar da tsaron al’umma.

Previous Post Next Post