Hukumar Kwastam, ta bayyana kama fatun jakuna da aka busar, masu nauyin kilogiram 13.6 da darajarsu ta kai naira biliyan 3.6 a Owerri, Jihar Imo.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar ranar Talata, an gano fatun jakunan ne a cikin wata kwantena mai tsawon kafa 40 da aka shirya domin fitar da su ƙetare, lamarin da ya sabawa dokar hana fitar da wasu kayayyaki daga ƙasar.
Kwamtrolan Kwastam na Sashen Ayyuka na Musamman (FOU) Zone C da ke Owerri, Abdullahi Balogun, ya ce jami’ansa da ke sanya ido ne suka bankado kayan bayan bincike na tsanaki da suka yi a cikin kwantenan.
Ya bayyana cewa fatun jakunan an nannade su a buhuna daban-daban, inda buhu ɗaya ke ɗauke da guda 9 ko 10. AN bayyana ƙididdigar fatun da aka kama da guda 3,022 – kowanne na da nauyin kusan kilogiram 4.5 – wanda nauyin su duka ya kama kilogiram 13,599.
Balogun ya ce an haramta fitar da fatar Jaki daga Najeriya saboda illarta ga halittu, da kare lafiyar muhallin, da kuma yadda ake amfani da ita wajen cin kasuwar dabbobin da ke cikin haɗarin karewa.
Balogun ya ce "Fatar jakunan da aka kama an shirya fitar da su ne ba bisa ka’ida ba, kuma darajar su a kasuwar duniya ta kusan dala 750 akan kowace fata – ko kuma dala 166.6 a kan kowanne kilogiram,".
Kana ya yaba da jajircewa da kuma ƙwarewar jami’an da suka gudanar da kamen, yana mai jaddada cewa ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamtrolan Kwastam, Bashir Adeniyi, hukumar za ta ci gaba da aiwatar da dokokin hada hadar kasuwanci na gwamnati da yaki da fataucin kayayyaki da aka haramta.
Balogun ya gargaɗi waɗanda ke da hannu a harkokin fataucin namun daji da kayayyakin da aka hana, da su daina kafin su faɗa tarkon hukuma.
Ya kuma ce hukumar za ta ƙara zage damtse wajen sanya idanu da tattara bayanan leƙen asiri da kuma gudanar da dabarun bincike da shawo kan masu laifi a fadin ƙasar.