Fiye da Mutum Miliyan Biyar Ambaliyar Ruwan Shekarar 2024 Ta Shafa – NEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa kimanin mutane 5,264,097 ne ambaliyar ruwa ta shafa a fadin Najeriya a shekarar 2024.

Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar, ta bayyana hakan yayin wata ganawa da wakilan Japan International Cooperation Agency (JICA) a Abuja, dangane da shirin tallafin gaggawa ga waɗanda ambaliya ta shafa.



A jawabin ta bakin Mataimakin Daraktan rage haɗurra na hukumar, Mista Simon Katu, Hajiya Umar ta ce ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 1,237, da rusha gidaje 116,172, kuma fiye da mutane miliyan 1.2 sun rasa matsugunansu.

“ An samu ambaliyar a jihohi 35, inda ta shafi gidaje, kayayyakin abinci, da muhimman abubuwan more rayuwa. Matsalar ta tsananta ne sakamakon rashin kyawawan magudanar ruwa a birane da sauyin yanayi,” in ji Katu.

A cewar bayanan da aka gabatar, kananan hukumomi 401 ne lamarin ya shafa, inda mutane 16,469 suka jikkata, gidaje 116,172 suka rushe da kuma  hekta miliyan 1.44 na gona  ambaliya ta lalata.

NEMA ta kuma yi hasashen cewa jihohi 12 da kananan hukumomi 43 na cikin  hadarin samun ambaliya a 2025, yayin da wasu jihohi 13 ke cikin jerin masu ƙarancin haɗari.

Hajiya Umar ta jaddada bukatar tashi tsaye da wayar da kan jama'a tun daga tushe, tana mai cewa hukumar ta faɗaɗa shirinta na ƙarfafa matakan gaggawa da wayar da kai a ƙananan hukumomi.

“Ba kamar da ba, yanzu mun kai shirye-shiryenmu zuwa kowacce jiha domin tabbatar dac wayar da kan al'umma kan shirin gaggawa tun kafin fuskantar Ibtila'i,” in ji ta.

Ta kuma kawo misalin ambaliyar Mokwa a jihar Neja, inda fiye da mutane 3,000 suka tagayyara, 1,005 suka rasa matsugunansu, sannan mutane sama da 100 suka mutu ko suka bata.

A ƙarshe, ta bayyana cewa NEMA na shirin gudanar  atisayen bada agajin gaggawa a jihohin Anambra da Kano, domin ƙarfafa ƙoƙarin tsare lafiyar al'umma da shirye-shiryen kare rayuka idan bukatar hakan ta tashi.

Previous Post Next Post