Kotu Ta Ci Tarar Wani Kamfanin Jima Sakamakon Laifin Gurbata Muhalli a Kano

Wata kotun majistare a Kano ta yankewa wani  kamfanin Jima na Globus Tannery da wani matashi mai suna Mubarak Yusuf, hukunci  sakamakon laifin karya dokokin kula da muhalli da lafiyar al'umma. 



Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta gurfanar da su a gaban kotu ta sanarwa da  a shafinta na Facebook a ranar Juma’a.

An kama kamfanin, wanda ke Chalawa, da laifin zubar da ruwan dagwalo da ba a tace ba, lamarin da ya sabawa dokar hana gurbatar muhalli ta jihar Kano ta shekarar 2022 da kuma dokar kiwon lafiyar jama’a ta 2019. Kotun ta ci kamfanin tarar ₦100,000 ko kuma daurin wata guda a gidan gyaran hali idan ya gaza biyan tarar.

A wani hukuncin na daban, kotun ta umurci Mubarak Yusuf da ya takaita amfani da keken dinki da janareto daga karfe 6 na safe zuwa 9 na dare, bayan samunsa da laifin haifar da hayaniya da ke hana makwabta barci.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir M. Hashim, ya yaba da hukuncin kotun, yana mai jan hankalin jama’a cewa duk wani nau’i na gurbatar muhalli zai fuskanci hukunci daidai da doka

Previous Post Next Post