Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, da ke jagorantar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ya bukaci a kara kaimi wajen dakile shan miyagun kwayoyi a dukkanin fannoni na rayuwar yau da kullum.
Marwa ya yi wannan kira ne yau Juma’a a Babban Masallacin kasa da ke Abuja, yayin sallar Juma’a da aka gudanar a matsayin wani bangare na bikin Ranar Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi ta Duniya ta shekarar 2025.
Shugaban na NDLEA ya jaddada cewa akwai hujjoji bayyanannu da ke nuna cewa rigakafi yafi magani fiye da gyaran halayen wadanda suke ta'ammali da miyagun kwayoyi.
A cewarsa, a karkashin jagorancinsa, NDLEA ta kama mutane dubu 66 da 85 tare da gurfanar da dubu 12 da 205, sannan ta kwace fiye da tan dubu 11,na miyagun kwayoyi, baya ga lalata gonakin wiwi da suka fi fadin kadada dubu 1 da 500.