NSCDC Ta Tura Jami’ai Sama da 3,100 Don Tabbatar da Tsaro a Sallah.

Rundunar tsaro da bada kariya ga fararen hula (NSCDC) reshen Jihar Kano ta bayyana cewa ta tura jami’ai sama da 3,100 domin tabbatar da tsaro yayin bukukuwan sallah Babba a fadin jihar.

Sanarwar da kakakin rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar, ta ce an tura jami’an tsaro zuwa wurare daban-daban kamar filayen Sallah da cibiyoyin yin nishadi da kasuwa, da sauran wuraren da ake ganin suna da muhimmanci wajen bada tsaro.

Kana an umarci jami’an da su tabbatar da cikakken tsaro kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan Sallah. Rundunar ta kuma ja kunnen duk masu neman tayar da zaune tsaye ko aikata laifuka cewa za a kama su tare da hukunta su yadda doka ta tanada.

NSCDC ta kuma bukaci jama’a da su rika bayar da rahoton duk wani motsi ko abin da suke zargin na rashin tsaro ga hukumomi, tare da bada hadin kai don ganin an gudanar da bukukuwan Sallah cikin  kwanciyar hankali da lumana.

Rundunar ta tabbatar da kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a wannan lokaci na bukukuwa sallah.

Previous Post Next Post