Gamayyar Jam’iyyun adawa na PDP, NNPP, CUPP, da sauran su na sukar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike.
Hakan na zuwa ne bayan ya fito fili ya bayyana shirinsa na jagorantar yakin neman zaben shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da kalaman Wike, inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar za ta aiwatar da dokokinta a kan ministar.
A nasa bangaren, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar CUPP, Mark Adebayo, ya bayyana Wike a matsayin “Magoyin bayan Tinubu”, inda ya zarge shi da kokarin wargaza jam’iyyun adawa.
Shima da yake magana kan wannan, Sakataren Yada Labarai na NNPP, Ladipo Johnson, ya ce shugaba Tinubu zai sha kaye a 2027 duk da amincewar Wike.
Ya kuma yi kira ga jam’iyyar PDP da ta mayar da ‘ya’yanta a karkashinta. Johnson ya ce ’yan Najeriya ne, a karshe ne za su tantance makomar Tinubu a zaben 2027, ba Wike ba.