REMASAB Ta Buƙaci Al'umma Su Rika sanar da ita Kafin Fito da shara.

 Hukumar Kula da Shara  da Tsaftar Muhalli ta Kano (REMASAB) ta yi kira ga mazauna jihar da su rika sanar da ita kafin gudanar da kowanne irin aikin tsaftar muhalli ko fitar da shara.

A cewar Mataimakin Daraktan Hukumar, Hon. Lameen Mukhtar Hassan, wannan matakin na da nufin kauce wa cunkoson ababen hawa tare da sauƙaƙa aikin kwashe shara cikin lokaci.

Mataimakin Daractan ya bayyana haka ne ta wani saƙo da aka wallafa a shafin Facebook na hukumar a ranar Talata.

Kiran ya biyo bayan wani aikin tsaftar muhalli na tsawon kwanaki biyu da aka gudanar a faɗin jihar, inda bayan kammala aikin, galibin tituna da manyan hanyoyi suka cika da shara da aka zubar ba tare da tsarin da ya dace ba.

Duk da cewa ana kara samun kira kan sanya dokokin tsaftar muhalli mai tsauri, wasu mazauna suna dora alhakin hakan kan rashin ingantaccen tsarin kwashe shara da kuma ƙarancin ababen  zuba shara a wuraren da suka kamata.

Masana sun yi gargadi cewa ci gaba da zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba na barazana ga lafiyar jama'a da ma muhalli.

Previous Post Next Post