Shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, Abdullahi Usman, ya bukaci maniyyata da su guji fita waje tsakanin karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma, saboda yanayin zafin kasar Saudi Arabiya.
A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin kasar Saudiyya ta hannun cibiyar kula da yanayi ta kasa (NCM) ta bukaci maniyyata da su yi taka tsantsan saboda yanayin zafi na rana zai kai daga digri 40°C zuwa 47°C.
Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Makkah a ranar Litinin din da ta gabata, shugaban NAHCON ya ce hukumar ta gudanar da wani taro da jami’an hukumomin jin dadin alhazai na Jahohi, inda suka amince da cewa dukkan maniyyata zasu kasance a cikin tantunansu na tsahon awannin da aka ayyana.
Tags:
Labarai