Tsohon Soja Ya Fada Hannun ‘Yan Sanda a Jihar Neja Bisa Zargin Damfara da Yin Sojan gona



Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani tsohon soja da aka kora daga aiki, Michael Musa, bisa zargin yin Sojan gona da kuma damfarar masu na’urar POS a sassa daban-daban na jihar.

Kakakin rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da yake sanye da kakin sojoji domin ya yaudari mutane da cewa har yanzu yana cikin aikin soja.

A bayanan ‘yan sanda, Michael Musa ya damfari wani mai POS a garin Bida zunzurutun kudi naira dubu 120,000. Haka kuma, ya ci amanar wani a Kataeregi inda ya karbi naira dubu 300,000 ta hanyar yaudarar sa da cewa jami’in soja ne.

A  baya-bayan nan, ranar 29 ga watan Mayu, Musa ya yi wa wani mai POS a kan titin Mandela da ke birnin Minna zamba har ta naira dubu 50,000.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike yayin da karin wasu mutane ke ci gaba da kawo korafe-korafen da suka shafi irin wannan damfara.

A karshe dai rundunar  'yan sandan ta jaddada aniyarta na ci gaba da yaki da masu yinSojan gona da sunan jami’an tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar.

Previous Post Next Post