Mummunar gobara ta tashi a kasuwar waya da ke Farm Centre a yau Juma’a, inda ta shafi shaguna 47.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:32 na rana, bayan da Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta samu kiran gaggawa daga al'umma.
Gobarar ta fara ne a bene na ƙasa na wani gini mai fadin kafa 700 x 400, mai ɗauke da shaguna 80.
Shaguna 20 na dindindin da 13 na wucin gadi sun ƙone a bene na ƙasa, yayin da shaguna 13 da wani shago ɗaya na wucin gadi suka ƙone a saman bene.
Jami’an hukumar kashe gobara sun yi amfani da motoci 5 wajen dakile wutar. Babu asarar rai ko raunuka da aka samu.
Sanadin gobarar ya faru fashewar baturin. Hukumar ta ce ana ci gaba da bincike.
Tags:
Labarai