Yariman kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya nuna matukar farin cikinsa kan yadda aikin Hajjin bana ya gudana cikin nasara, yana mai jaddada cewa wannan nasara ta samo asali ne daga himma da jajircewar Kasar Saudiyya wajen hidimtawa Masallatai Masu alfarma da kuma maraba da bakin Allah.
Ya kara da cewa, Nasarar da muke gani a yau wajen hidima ga bakin Allah ita ce sakamakon kokarin Kasarmu mai albarka, wajen hidima da bada kulawa ga Masallatan Makkah da Madina masu alfarma, da Sauran wuraren ibada da su kansu masu ziyara.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Saudiyya za ta ci gaba da zage damtse wajen saukaka rayuwa da bukatun mahajjata, yana cewa: “Za mu ci gaba da ba da samar da abu uwan ci gaba domin jin dadin bakin Allah.”Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana hakan ne a wani taron gaisuwar Sallah da aka gudanar a Fadar Mina, inda ya karbi gaisuwar Sallar a madadin Sarki Salman bin Abdulaziz.
Taron ya samu halartar manyan 'ya’yan sarauta, babban Limamin Saudiyya, manyan jami’an gwamnati, kwamandojin tsaro da ke kula da harkokin hajji, da kuma baki daga kasashen kungiyar hadin kan Gulf (GCC).
Yariman ya kuma nuna gamsuwarsa da gudunmawar ma’aikatan gwamnati da masu aikin sa kai daga sassa daban-daban, bisa yadda suka taka rawar gani wajen tabbatar da cewa mahajjata sun gudanar da ibadarsu cikin aminci, lafiya da nutsuwa.