NAFDAC Ta Gargadi 'Yan Najeriya Kan Hadarin Amfani da Wasu Kayayyakin Goge Jiki da Turaren Dove da EU Ta Haramta

 

Hukumar  NAFDAC ta fitar da gargadi ga 'yan Najeriya game da hadurran da ke tattare da wasu kayayyakin kamfanin Dove da Hukumar Tarayyar Turai (EU) ta haramta.

NAFDAC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai lamba 018/2025 da ta fitar mai taken “Gargadi Kan Haramta Sabulun  da Turaren Dove Saboda Guba Nau’in Butylphenyl Methylpropional”.

A cewar hukumar, kayayyakin da abin ya shafa sun kunshi sinadarin 2-(4-tert-butylbenzyl) propionaldehyde, wanda aka fi sani da BMHCA, kuma wannan sinadari an haramta amfani da shi a cikin kayayyakin kwalliya a Tarayyar Turai saboda yana da illa ga lafiyar dan Adam.

“Kayayyakin ba su dace da ka’idojin kayayyakin kwalliya na EU ba, saboda sun kunshi sinadarin BMHCA wanda ke da hatsari ga  haihuwa, yana iya cutar da jarirai cikin Mahaifiya, kuma yana haddasa rashin lafiyar fata,” in ji sanarwar NAFDAC.

NAFDAC ta lissafa kayayyakin da abin sun hada:

Dove Exfoliating Hand Soap (100g) – Barcode: 8710447439227

Dove Deo Go Fresh 50ml – Batch Number: 9212174

Dove Invisible Dry 50ml – Batch Number: 9183646

Dove Men + Care Silver Control Spray 150ml – Batch Number: 62867LD

An ce an samar da wadannan kayayyaki ne a Italiya da Birtaniya, kuma babu wani daga cikinsu da ke cikin rajistar NAFDAC.

Hukumar ta kara da cewa shigo da sabulan Najeriya haramun ne, bisa dokokin kayayyakin da aka hana shigo da su a kasar, tare da karin bayani cewa wadannan kayayyaki ba su da damar samun kudin musaya daga wajen gwamnati don shigo da su cikin kasa.

NAFDAC ta bukaci masu shigo da kaya, masu rarrabawa da masu sayarwa da su kula da yin kaffa-kaffa, kada wadannan kayayyaki su shiga cikin Kasuwannin Najeriya.

“Kayan basa cikin tsarin kayayyaki da ke runbun bayanan hukumar, ko na masu shigowa da su, sayarwa,. Duk wanda ke da su a hannunsa ya daina amfani da su ko sayarwa, kuma ya kai su ofishin NAFDAC mafi kusa,” in ji sanarwar.

NAFDAC ta kuma bukaci likitoci da masu amfani da kayayyakin kwalliya su rika ba da rahoton duk wani kaya  mara kyau.

A karshe, hukumar ta jaddada kudirinta na kare lafiyar al'umma tare da ci gaba da sanya ido kan kayayyakin kwalliya a kasuwanni Najeriya domin hana yaduwar kayan da ke da hadari.

Previous Post Next Post