Fiye da gidaje 110 ne suka lalace sakamakon wata guguwa mai karfi da ta afka wa kauyen Chirin da ke ƙaramar hukumar Bunkure a jihar Kano a Laraba makon da ya gabata, .
Rahoton wannan mummunan lamari ya fito ne a cikin wata takarda da aka mika wa Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dokta Muhammad Isa Umar, a yayin zaman fada da aka gudanar ranar Litinin.
Mai Martaba Sarkin Rano ya nuna jimaminsa tare da yi wa mazauna kauyen addu’a, yana mai roƙon Allah Madaukakin Sarki ya kare su daga irin wannan ibtila’i nan gaba. Haka kuma, ya bayar da umarnin a tura rahoton zuwa ga shugaban ƙaramar hukumar Bunkure don ɗaukar matakan gaggawa na tallafi da agajin gaggawa.
Da yake magana da manema labarai a fadar Sarkin, Hakimin Chirin, Alhaji Nura Usman Iliyasu, ya bayyana guguwar a matsayin abin ban tsoro da ba a taɓa fuskanta irinta a tarihin kauyen ba.
